Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuna cewq mota mai sulke da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba shi ta taimaka masa ya tsallake harin bam da aka kai masa a Kaduna a shekarar 2014.

Ya bayyana haka ne a wani shirin tarihinsa na musamman, mai taken‘Essential Muhammadu Buhari’, wanda aka nuna a jiya Lahadi.

TheCable ta tuna cewa a watan Yulin 2014, ayarin motocin Buhari ya gamu da harin bama-bamai da suka afku a yankin Kawo na jihar Kaduna.

Buhari, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a lokacin, ya ce shi ne aka kai wa harin bam É—in, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Da ya ke tsokaci kan lamarin a cikin shirin, Buhari ya ce Rabiu Kwankwaso, wanda shi ne gwamnan Kano a lokacin, ya ba shi kyautar motar da yake ciki a lokacin da fashewar ta faru.

“Kwankwaso ya kyauta min da ya bani kyautar motar nan. Ya ba ni mota kirar Land Rover mai sulke,” inji Buhari.

“Ya ce kamata na yi amfani da ita saboda a yanayin kalubalen da na ke fuskanta, za a iya samun wasu mugaye su hallaka ni.

“Ina kan hanya ta ta zuwa Kano daga Kaduna a cikin waccan motar jeep sai wata mota ta so ta yanke mu amma sai Æ´an rakiya ta su ka tare ta, shine nan take su ka tashi bam din.

“Da na duba, sai na ga sassan jikin mutane. Babu daya daga cikin mu da ya ji rauni a cikin motar. Amma ko ta yaya na ga jini a jiki na saboda yawan mutanen da bam din ya kashe a wajen,” in ji Buhari