Budaddiyar wasika zuwa ga Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa.


Daga Dr. Abdulaziz T. Bako.


Bayan gaisuwa irin ta musulunci tare da girmamawa, ina fatan kana cikin koshin lafiya.


Mai girma Waziri, hakika a tsawon shekarun da ka yi kana siyasa ka nuna jarumta da karfin hali a kudirinka na zama shugaban kasa. Sai dai akwai wasu tuhume-tuhume tsakaninka da talakawan Najeriya da har yanzu suka sanya wannan kudiri naka ya kasa kaiwa ga ci.


Mai girma Wazirin Adamawa, mutane suna jifanka da zarge-zarge da tuhumen-tuhume na cin hanci da rashawa. A kwanan nan an fitar da faya-fayan audio inda aka ji wata murya da ko kadan bata da bambanci da taka tana bayani akan yadda kuke siddabaru a kasa gane yadda kuke yin almundahana da dukiyoyin al'umma. 


Ya mai girma Waziri, har yanzu talakawan Arewa ba su manta da yakar shari'ar musulunci da ka rika yi lokacin kana mataimakin shugaban kasa ba. Dadin dadawa mutane suna ci gaba da tuhumarka da raina talakawa ta yadda magana ke maimaituwa cewa ka taba cewa Allah ma ba ya amsar addu'ar talaka. 


Mai girma Waziri wadannan tuhume-tuhume ko shakka babu sun dade suna bibiyarka kuma sun sanya har yanzu talakawa, musamman na Arewa, hankalinsu ya kasa amintuwa da su dauki amanar jagoranci su baka.


Mai girma Waziri, ko da babu wadannan tuhume-tuhume. Akwai maganar shekaru. Girma ya iso maka. Kuma a halin da Najeriya take ciki tana matukar bukatar mutum mai jini a jika ya jagorance ta. Yanzu lokaci ne da ya kamata ka hutar da kanka ka kasance daya daga cikin masu bayar da shawara akan yadda zaa tafiyar da kasa ta samu ci gaba. 


Ya Mai girma Waziri, Engineer Rabiu Musa Kwankwaso, mutum ne wanda talakawa suka aminta da shi, duba da yadda ya dauki shekaru yana gina yayan talakawa ya sauya musu rayuwarsu zuwa rayuwa mai inganci da daraja. Masana da yawa suna ikirarin cewa kaf shugabannin Najeriya da suke raye yanzu babu wanda ya bautawa harkar ilimi a Arewa kamar Kwankwaso. 


Bisa wadannan dalilan ne mu ke neman alfarmarka da ka taimaki al'ummar Najeriya ka janye masa takarar nan. Dukanninmu mun yarda cewa barin jam'iyyar APC ta ci gaba da mulki a Najeriya ba karamin babban kuskure bane. Don haka ya zama tilas a zo a hada karfi da karfe a kayar da wannan jam'iyyar ta APC. 


Ya mai girma Waziri, Kwankwaso mutum ne mai cika alkawari. Dukkan wani alkawari da zaku yi da shi a wurin yarjejeniyar da zaku yi da shi ta janye masa takara, mu da mu ka san waye Madugu, mun tabbatar da cewa ba zai kaucewa wannan yarjejeniyar ba. Mun tabbatar da cewa duk wani alkawari da Madugu zai yi a wurin wannan yarjejeniyar zai cika su. Kofar Madugu a bude ta ke a ko wane lokaci don hada gwamnatin had'aka.


Da wannan muke rokon mai girma Waziri ya dubi koke-koken talakawan Najeriya ya janyewa mutum daya tilo da kowa ya yarda cewa yana da nagarta, kuma yana da kyakkyawan tanadi da burin inganta rayuwar talaka, shine Madugu. Engineer Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.


Sunana Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD.