Bayan ziyarar Tinubu, yan sanda sun kama yan Daba 61 da muggan makamai a Kano


By


 Abubakar  Lecturer


January 6, 2023


kokarinta na ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a lokutan zaɓe, rundunar yan sanda ta jihar Kano tace ta samu nasarar cafke wasu gungun matasa guda 61, wadanda ake zargin yan Daban siyasa ne.


Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ne bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakin hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda yace an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da ake tsaka da gudanar da taron siyasa ranar 4 ga wata a filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata.


Sanarwar ta bayyana cewa, an kama su ne tare da Wuƙaƙe guda 33, Adduna guda 8, Almakashi guda 6, ƙunshin daurin tabar wi-wi guda 117, da kuma kwalaben magani da ƙwayoyi.


A saboda haka ne, kwamishinan yace zasu gurfanar da matasan a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka, tare da yin kira ga jami’an tsaro, bijilanti, yan jarida, Æ™ungiyoyi da kuma shugabannin al’umma da suka cigaba da addu’a tare da sanya idanu da bawa jami’an tsaro goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.


Source: NASARA RADIO