Wannan matashin Dan asalin jihar Zamfara ne ranar litinin data gabata Ina zaune a office da gefin magariba sai naji Ina sha'awar Awara shine fa na tare dan a daidai sahu na hau domin ya kaini inda zan samo Awara bayan na sayi Awara Ina kan Hanyar komawa sai hango wannan Mai Keke napep na zuwa sai na sa Masa hannu sai ya tsaya bayan ya tsaya sai naga Keke napep dinsa duk an lika hotunan Madugu sai nace dashi kaima masoyin oga ne kenan?
Sai yace Dani ai Mai gida ni da kake Gani nan wallahi ban taba yin katin zabe ba sai wannan shekara Kuma wallahi nayi wannan katin zabe ne domin na zabi Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a lokacin zabe mai zuwa.
Sai nace dashi mayasa zaka zabi Kwankwaso?
Yace Dani domin Nayi Imani ko ban anfana da mulkinsa ba 'ya 'yan talakawa Irina zasu anfana, Ni Dan jihar Zamfara ne Amma Ina Jin labarin irin yadda yake taimakon 'ya 'Yan talakawa don haka dole ne Yanzu mu 'ya 'yan marasa karfi mu hadu mu tallafa Masa Zuwa ga samun Nasara.
Nace dashi kana Facebook?
Sai yace Dani wallahi ni yanzu ma ko wayar bani da ita.
Tabbas naji Da'di sosai da ya kasance talakawa 'yan dangwale sun fuskanci manufofin Kwankwaso a kansu...
Daga Munir Abdullahi Usman ✍️
0 Comments
Post a Comment