A yankin Karamar Hukumar Gbako ta Jihar Neja, wasu iyayen Amarya sun bukaci waliyyan Angon da za daura aurensa da ’yarsu da su mayar da takardun N1,000 da na N5,000 din da suka kai a matsayin kudin sadaki.


Iyayen angon dai sun kai kudaden da ba a bayyana adadinsu ba a matsayin na sadaki da na sauran saye-saye a shirye-shiryen bikin, amma iyayen amaryar sun yi korafin cewa ba su da bukatar kashe duka kudaden kafin nan da ranar 31 ga watan Janairu, wa’adin da CBN ya bayar ba daina amfani da su, sannan ba su da asusun bankin da za su zuba su a ciki.


Hakan ne ya sa suka ki karbar tsoffin kudaden, tare da bukatar a ba su sababbi matukar ana son a daura auren, kamar yadda wani dan uwan Ango ya bayyana.