Michael Achimugu wani tsohon hadimin Atiku Abubakar ne wanda suka dade suna mu'amala da shi a matsayin daya daga cikin masu kula da wallafe-wallafe da na kare muradai da sunan Atiku a kafofin yada labarai da na sada zumunta.


A wani faifen video da shi wannan dan taliki ya saki. Ya yi jawabi dalla-dalla akan mu'amalar da ke tsakaninsa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Ya bayyana cewa a zamansa a matsayin hadimin Atiku ba shi da wata matsala da shi Wazirin Adamawar, amma kawai yana gani cewa lokaci ya yi ne da ya kamata ya bayyanawa yan Najeriya irin bakar illar da ke tattare da zaben Atiku a matsayin shugaban kasa. Saboda haka ne ma ta ce dan kadan kawai zai tsakurawa yan Najeriya daga cikin irin ta'asar da Atiku ya tafka lokacin yana mukamin mataimakin shugaban kasa. Zai yi wannan ne kuma kawai don baiwa talaka damar sanin wanene Atiku.


Amma sai dai Mr. Michael ya yi kwakkwaran kashedi ga masu kula da al'amuran Atiku akan cewa su bi shi a hankali, domin kuwa sirrukan da yake da su a kan Atiku, Allah ya yi yawa da su, kuma da zai saki rabinsu, da babu mamaki Najeriya ta shiga radan in da bata taba shiga ba tunda aka bata mulkin kanta a shekarar 1960.


Tsohon hadinin na Atiku ya ce ya baiwa lauyoyinsa umurnin cewa ko fatar jikinsa aka tsakura saboda Atiku toh su fara sakin bayanan da ya boye.


A watan Yuni (June) na shekarar 2018 ne aka fara yada labarin cewa Atiku Abubakar ya karbi cin hancin Naira miliyan 100 a jannun tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, a lokacin shi Atikun yana matsayin mataimakin shugaban kasa. A matsayin Michael Achimugu na hadimin Atiku sai yake kokarin yi masa gambayoyi akan yadda gaskiyar abin yake domin ya san yadda zai yi rubutu ya kare Atikun, wanda wannan dama a al'adance haka ake yi.


Sai dai da ya tambayi Atikun sai ya amsa masa tambayarsa ta email da cewa ai kudin ( Naira Miliyan 100) din da ake zargin ya karba a hannun Joshua Dariye, an tura su ne cikin wani account da Atikun ya kira SPV. Shine sai hadimin nasa, Michael, ya ce shi bai gane ma'anar wannan kalma ta SPV ba. Shine sai Atiku ya kirawo shi wannan hadimi takanas ta Kano a waya domin ya zayyane masa ma'anar ita wannan kalma ta SPV. Shi kuma Mr. Achimugu ya fara nadar sautin Atikun.


Atikun ya fara da cewa ita wannan kalma ta SPV tana nufin Special Purpose Vehicle, wato Wata Na'urar Aike ta Musamman. 


Atiku ya ci gaba da cewa lokacin da suka hau mulki shi da Obasanjo, ya baiwa Obasanjo shawarar cewa ya guji tsunduma cikin al'amuran rashawa gaba gadi ko firi falo. Atikun ya ke cewa ya nunawa Obasanjo cewa idan zaa yi harkar da ta shafi rashawa to su rika sakayawa suna bin wasu dabaru da duk yadda zaa yi ba zaa iya ganewa cewa suna da alaqa da wannan rashawar ba. 


Lokacin da maganar karbar wannan miliyan dari ta tashi sai Atiku ya nemi cewa shugaban kasa Obasanjo a lokacin cewa ya bashi sunayen mutum uku da ya aminta da su. Sai shi Atikun ya sa aka bude musu kamfanunuwa na bogi guda uku.


Atikun ya ci gaba da cewa su amfanin wadannan  kamfanunuwa na bogi shine, idan aka tashi yin wata harkalla da ta shafi satar kudin gwamnati, sai a bayar da kwangila, sai su wadannan kamfanunuwa su zo a matsayin yan ka yi na yi (consultants)  sai a basu ladan aikinsu. Su kuma su Atikun idan an turawa kamfanin wannan kudi sai su kwashe kudin su raba tsakaninsu. 


Atiku ya ci gaba da cewa shi ya sa lokacin da maganar ta taso EFCC ta yi iya binciken duniyar nan da zata yi ta kasa kama shi da laifi saboda kwata-kwata babu sunansa a cikin wadanda suka kafa kamfanin, duk da cewa shi ya sa aka kafa kamfanin na boge.