Dan takarar gwamnan jihar Katsina kalkashin jam'iyyar NNPP engr.Nura Khalil yayi alkawalin cewa idan al'ummar jihar suka zabe shi zai bunkasa hanyoyin ssmun kudin shiga daga arzikin da Allah ya fuwace ma jihar domin inganta rayuwar  su


  Nura Khalil yayi wannan alkawalin ne a wajen taron kandamar da gangamin yakin neman zaben yan takarar jam'iyyar wanda ya gudana a karamar hukumar Mashi dake jihar


 Ya bayyana cewa jihar Katsina tana bukatar mutum mai tunani da kaifin basira da zaiyi amfani da ilmin sa wajen inganta  tattalin arzikin ta ta hanyar zakulo albarkatun da Allah ya fuwace mata domin bunkasa su da nufin samun kudade domin inganta rayuwar al'ummar jihar


"Saboda halin da aka jefa jihar Katsina ciki a halin yanzu, ya zama wajibi ga duk wanda zai nemi kujerar gwamna ya kasance wanda zai iya kawo ma jihar hanyoyin kudin shiga domin ayi ma mutane aiyukan da zasu inganta rayuwar su".


"A nan karamar hukumar Mashi muna da arzikin tataccen hasken rana da babu irin sa a fadin kasar nan wanda zamuyi amfani dashi wajen kafa kamfanin hasken wutar lantarki namu na kanmu wanda zai rika samarwa jihar biliyoyin kudade a duk shekara kamar yadda masana suka tabbatar",inji Nura Khalil.


Kamar yadda ya bayyana hakan zai sa jihar tayi ban kwana da jiran daunin wata wata daga gwamnatin tarayya tare da bata damar gogayya da jihohi masu arziki wajen tara kudin shiga na cikin gida da za'a rika amfani dasu domin inganta rayuwar al'ummar jihar


Engr. Nura Khalil ya kuma bayyana aniyarsa ta samar da wani tsari da zai baiwa matasa damar samun guraben aikinyi ta hanyar tallafa masu da hanyoyin da zasuyi dogaro da kansu a maimakon jiran gwamnati ta basu aikin yi


 "Za mu yi amfani da tsarin domin koyama matasa sana'o'i da kuma tallafama kanana da matsakaitan masana'antu domin samawa matasa da mata hayoyin dogaro da kai", dan takarar yayi alkawali.


 Ya kuma yi alkawalin inganta bangaren ilmi tare da tabbatar da kowane yaro a jihar yana samun ilmi kyauta tare da biyan kudin jarabawa ga kowane dalibin sakandire domin tabbatar da sun cigaba da fadada ilminsu a manyan makarantu


Yace, "Za mu samar da wani asusu na musamman da zamu yi amfani dashi wajen tabbatar da yaran mu sun samu ingantaccen ilmi a fadin jihar Katsina".


Dan takarar gwamnan wanda ya yaba da irin kyakkyawar tarba daga magoya bayan jam'iyyar ta NNPP a wajen taron ya bukace su da suje gida su adana katin zaben su su jira lokacin zaben na 2023 mai zuwa su zabi jam'iyyar NNPP a dukkanin matakai domin inganta rayuwar su 


Taron gangamin ya samu halartar jagoran kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP engr. Rabi'u Kwankwaso wanda ya samu wakilcin dan takarar gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf da shugaban jam'iyyar na jihar Katsina da yan takarar kujeru daban daban hadi da dimbin magoya baya da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ta NNPP a jihar ta Katsina.


A lokacin taron an kaddamar da yan takara tare da basu tutoci domin shiga lungu da sako da nufin nema ma jam'iyyar NNPP kiri'un samun nasarar zaben na 2023 mai zuwa.