Rundunar 'yan sandan Iran ta kama wasu 'yan ƙwallon ƙafar ƙasar bisa zarginsu da shirya bikin shiga sabuwar shekara a birnin Tehran na ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.
BBC ta rawaito cewa wasu daga cikin waɗanda aka kaman sun haɗar da tsoffin 'yan wasa da kuma 'yan wasan da ke taka-leda a yanzu.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim bai bayyana sunayen 'yan ƙwallon da aka kaman ba, bai kuma yi ƙarin bayani game da ƙungiyoyin da 'yan wasan ke taka wa leda ba.
Rahotonni sun ce wasu daga cikin 'yan wasan na cikin halin buguwa a lokacin da aka kama su.
A ƙasar ta Iran dai ana ɗaukar ire-iren waɗannan bukukuwa - waɗanda mata da maza ke cakuɗuwa - a matsayin haramun.
Ana yi musu kallon abubuwan da ke gurɓata tarbiyyar matasa a ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama a ƙasar sun kira matakin kamen da 'yan sandan ƙasar suka yi wa matasan a matsayin take haƙƙinsu da sirrinsu.
0 Comments
Post a Comment