Wata kotun majistare a Kano ta tasa keyar Tasiu Abdullahi zuwa gidan yari har sai an yanke hukunci kan neman belinsa.


A kwanakin baya ne ‘yan sanda su ka kama Abdullahi, mai shekaru 45, da katinan zabe na dindindin guda 29, mallakar wasu al’umma a karamar hukumar Dawakintofa ta jihar Kano.


Lauya mai shigar da kara, Hadiya Ahmad, ta ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin da ya sabawa sashe na 22 na dokar zabe ta 2022.


Sai dai Abdullahi ya musanta aikata laifin.


Don haka lauyansa MB Baba ya mika bukatar neman belinsa, amma mai gabatar da kara ya ki amincewa da bukatar.


Daga nan ne Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Saad-Datti ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan neman belin wanda ake zargin, sannan ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma ɗin a gidan yari.