Da amaryar da angon dukkanin su marayu ne wadan da suka tashi a gidan marayu na Nasarawa tun suna Yara.


Yau an daura musu Aure Kuma anyi biki kamar yadda akeyin bikin Yayan dangi karkashin jagoranci kwamishiniyar mata Malama Zahra'u.


Amarya ta shiga da kafar dama, domin kuwa a yau din wani bawan Allah Amb Yunusa Yusuf Hamza shi kuma ya samarwa angon aikin yi, 


Muna rokon Allah ya basu zaman lfy, ya albarkaci rayuwar auren su, ya dawwamar da farin ciki a tsakanin su.


Shi Kuma wannan bawan Allah da ya bawa ango aikin yi,

 Allah ya saka masa da alkhairi ya kara masa kwarin gwiwa akan irin wannan hidima. 


Wlh har Kuka nayi a Boye saboda Ina tunanin yadda suke ji a lokacin bikin su ba tare da iyaye su ba


Daga Nadiya Ibrahim Fagge