Hukumomin sojin Najeriya, hedkwatar tsaro da ke Abuja, sun tabbatar da cewa wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Litinin ta shafi hawa na biyu na DHQ da ke Twitter
Wannan gobara dai ta tashi ne a hawa na biyu na hedkwatar, ya zuwa yanzu kuma ba a san musabbabin tashinta ba.
An tattaro cewa, jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya da sojojin da ke wurin sun yi kokari wajen ganin sun dakatar da yaduwar wutar.
Daraktan yada labarai na tsaro a Najerya, Manjo Janar Jimmy Akpor ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kara da cewa, an yi nasarar kashe wutar kuma an tattara dukkan ma’aikatan da ke cikin ginin.
0 Comments
Post a Comment