📖 Aisha Bridget Lemu Shahararriyar marubuciyar litattafan addinin Musulunci ce haifaffiyar Birtaniya Kuma mazauniyar birnin Minna a taraiyar Najeriya. An haifeta a 1940, Kumar ta karbi musulunci a 1961, ta rasu a garin minna na jahar Neja ranar 5 ga Janiru na 2019.
📖 Lokacin da tana yar shekara goma sha uku (13), ta fara yin tunani na canza addini kuma ta fara nazarin sauran addinai, cikinsu har da addinin Buddha da na Hindu.
📖 Ta yi karatu a Jami’ar London Makarantar koyan Al’adu da harsunan kasar sin da Africa wato school of oriental and African studies (SOAS), a inda ta mai da hankalinta ga tarihin kasar Sin, da al’adun su.
📖 Ta hadu da dalibai Musulmai a wannan Jami’a ta (SOAS) waÉ—anda suka ba ta littattafan addinin musulunci ta ke karantawa, kuma ta karbi Musulunci a Cibiyar Al’adu ta Musulunci a shekarata 1961,
📖 A shekarar farko ne a kartunta ta bada gudunmawa wajen samar da kungiyar dalibai Musulmai a SOAS, a jami’ar ta London kuma itace sakatariyar kungiyar ta farko a makarantar.
📖 Bayan ta kammala karatun ta daga SOAS, Aisha ta tafi karatun digiri na biyu don koyan turanci kuma a lokacin ne ta hadu da mijinta, Sheikh Ahmed Lemu, wanda yake karatunsa a wata koleji a Jami’ar London kuma ya shiga cikin Ayyukan Musulunci a makarantun da suke yankin na london.
📖 Bayan da ta samu takardar shaidar gama digirinta na biyu a makarantar, ta koma Kano a watan Agustan, a shekara ta 1966 ta fara koyarwa a Makarantar Nazarin Larabci a, inda Sheikh Ahmed Lemu ya yi aiki a matsayin shugaban makarantar.
📖 Sun yi aure da Sheikh Ahmed Lemu a watan Afrilun shekara ta 1968, Aisha ta zama matarsa ta biyu.
📖 Daga baya sai ta koma Sokoto don ta zama shugabar makarantar Kwalejin ‘Yan mata ta gwamnati a sokoto.
📖 Sheikh Ahmed Lemu shine babban kadi na kotun daukaka kara na shari’a a Nija lokacin da aka kafa ta a shekara ta 1976, Aisha kuma ita ce shugabar babbar makarantar malamai mata a Minna har zuwa 1978.
📖 Ma’auratan biyu sun kafa Qungiyar Ilimin Musulunci wato Islamic Education Trust (IET) , wanda ke aiki a yanzu a cikin jihohin Najeriya da ke da ofisoshi da kuma É—akin karatu, da masu wallafawa, tare da makarantun primary da sakandare da kuma makarantar manyan mata.
📖 Aisha Lemu na daya daga Cikin memba na Cibiyar Nazarin Musulunci, wanda Cibiyar Nazarin Ilimi ta Nijeriya ta kafa, wanda zai sake nazarin tsarin ilimin Musulunci na kasa a matakai daban-daban.
📖 A shekara ta 1985, Aisha Lemu ta kafa kungiyar mata Musulmai a Najeriya (FOMWAN) tare da sauran mata Musulmai, kuma an zabe ta a matsayin shugabar musulmai mata ta kasa ta farko, kuma tayi shekaru hudu.
📖 Ta wallafa littafai da dama a fannin addinin Musulunci da ilimi wadanda aka rika amfani da su a makarantun sakandare na Najeriya.
📖 Malama Aisha ta rasu a ranar Asabar 5/1/2019, tana da shekara 79 da haihuwa bayan ta yi wata gajeruwar jinya.
📖 Malama Aisha ta bada gaggarumar gudun mawa a addini musulunci musammanma ta wajen rubuce-rubuce.
📖 Wannan babban rashi ne da musulmai muka yi na kundin ilimi mai muhimmanci wanda ba ya misaltuwa, idan mukayi duba da cewa karbar Musuluncin tayi, kuma Baturiya ce, amma ta tashi tsaye domin haskaka duhun jahilci ta hanyar amfani da hasken Musulunci.
📖 Nuruddeen Lemu, dan fari na marigayiya Aisha Lemu, yace abinda zai fi kewa game da mahaifiyar shi shine yanda ta dauki rayuwa da sauki ko a lokutan kalubale.Nuruddeen Lemu, dan fari na marigayiya Aisha Lemu, yace abinda zai fi kewa game da mahaifiyar shi shine yanda ta dauki rayuwa da sauki ko a lokutan kalubale.
📖 "Mahaifiya ta uwa ce ta gari da Allah ya bamu. Yanda ta dau rayuwa daban ne. Duk yanda kake kallon matsala ita ba haka take kallon ta ba. Ita tunanin ta yanda zamu rayuwa da wannan, ya kuma zamu cigaba. Ita gareta a rayuwa babu wata matsala," inji shi.
📖 Muna rokon Ubangiji Allah ya gafarta mata yasa aljannan ce makomarta ya albarkaci zuriyarta.
Daga Saliadeen Sicey
#danmusatech
0 Comments
Post a Comment