Ina jan hankalinku kuyi abin da ya dace idan kunje. "Abin dayasa na samar da wannan gidauniyar ta Kwankwasiyya Development Foundation, "Nasan wata rana bana raye, ayanzu nafi karfi ci da sha da kuma sutura.
babban burina shine! yanda 'Yayana suke karatu a makarantu masu kyau musamman na kasashen waje, haka nake so naga Dan talaka shima ya samu dama, na tabbata ilimin ku yafi gonakina da filayena muhimmanci, shiyasa nasai da wasu daga cikin kadarorina kuma na bude gidauniya domin Jama'a suma su taimaka, mu turaku Kasashen Duniya, ina da yakinin duk cikin ku babu mutumin banza,
Domin duk wanda zai samu sakamako mafi daraja a makarantun gaba da sakandire babu shakka yana da baiwar da idan yasamu dama zai amfanar da Al'umarsa da addinin sa.
Ina mai jan hankalinku kuyi abin daya dace ku fitar da iyayenku kunya muma damuka turaku kufitar damu kunya, ina addu'a Allah yayi muku albarka. Wannan ya farune lokacin da Gidauniyar Kwankwasiyya zata tura Dalibai dari uku da saba'in Kasashen ketare a shekarar 2019 a gidan sa dake Milla road a Jihar Kano
Wannan nasihar da Madugu yayiwa Daliban itace tasani hawaye, alokacin mafiya yawan Shugabanni suka zurme da son duniya da kece raini ta hanyar banbanta Y'ayansu da Y'ayan Talakawa da tara abin duniya kamar basa tunani zasu mutu.
Ya Allah kasan abin dake zuciyar bawanka Sanata Kwankwaso ka bashi Shugabancin Najeriya kuma kayi masa Jagoranci akan mulkinsa sabo da Shugaban Halitta Muhammadarrasulillah.🙏🙏🙏
0 Comments
Post a Comment