A duk lokacin da mutum yayi maka alheri ko sanadiyyar samun alheri ya kamata ako yaushe ka tuna da wannan alherin to mafi ƙyautatuwar abinda zaka yi masa shine kagode masa domin ba kowa ne yake iya isar da alheri ga wani ba. Haka ɗabi'ar musulmi ta dace duba da yadda jan hankali yazo akan maganar godiya a cikin littattafan musulunci.
Mutane suna yawan hakaito cewa Kwankwaso yayi sanadiyyar ilmintar da ya'yan talakawa har da na masu hali ƴan asalin jihar Kano da ba za su faɗu ba saboda yawansu. Musamman wanda aka kai ƙasashen waje. Idan kana jin labarin wasu zaka san abun babbane sosai. Duk wanda yaje wata ƙasar yayi karatu ƙyauta yasan irin daɗin da mutum yake ji a ransa idan yaga yana karatu kuma baya biyan ko tasi.
A cikin dukkan masu hakaito labarin farin cikinsu ko na abokansa banji wani ya faɗi ɗaya abun me matuƙar muhimmanci da shi ma adaidai wannan lokacin ya samu Kano ta hanyar Kwankwason ba. Ɗan saurara nasan ilmi yana da matuƙar muhimmanci. Haka ma arziƙi yana da amfaninsa me tarin yawa. Yadda Kwankwaso yayi sanadiyyar samun masu karatu a Kano da Nigeria haka yayi sanadiyyar samar da ƙarin masu arziƙi. Kai zan iya cewa yawan miloniyas a Kano ya ƙaru tun wannan lokacin. Domin kuwa inde mallakar Naira miliyan ɗaya ko sama da haka shine ya ke sa a kira mutum da miloniya to kuwa Kano ta samu ƙarinsu birjik. Domin arziƙin mutane ya haɓaka musamman da zarar sun dawo gida bayan kammala karatunsu sun ɗan canja ragowar dalolinsu/Lira/Ringgit/ Dirham/Yuan.
Tattalin arziƙin samari ya haɓaka wanda haka ba ƙaramar nasara ba ce a cikin al'ummar jihar Kano. Kaga ansamu riba biyu ga karatu ga kuɗi. Ƙaruwar tattalin arzikin samarinnan ba ya tsaya bane a kansu kaɗai. Yan'uwa da al'ummar Annabi duk ta samu na ta alherin. Wasu sun samu jari, sun mallaki gidaje, filaye, abun hawa. Kai harda masu aure. Abun farin ciki ko ta ina. Har yanzu mutane suna girbar wannan alherin.
Allah mungode maka da ni'imar samar da Kwankwaso da kayi a lokacin mu.
0 Comments
Post a Comment