NASIHA: Mu Yi Kokarin Rabuwa Da Iyayenmu Lafiya, Domin Ba Ka Gane Girman Rashin Su Sai Ka Rasa Su
Daga Zaharaddeen Ganduu
Tabbas rashi mahaifa babbar masifa ce, domin iyaye gata ne kuma garkuwa ga ne 'ya'yansu.
Duk waɗanda suke da iyaye ba su ganin darajar su ko ƙimarsu sun yi asarar, ina ganin sakacin waɗanda ke tare da mahaifansu ke a raye amma ba su iya nuna ƙoƙarinsu wajan ganin sun faranta musu rai.
Waɗanda ke irin haka da za su san cewa, mu'amalantar iyaye ƙaramin zango gareshi, karku nesanta da su, domin muddin akace sun rasu, wallahi damar neman al'barkarsu ta suɓuce har abada a gareku.
Idan baka kyautata ma iyayenka ba suka ji daɗi ba, dole ka yi ma matarka ko abokanka waɗanda ba tabbas ɗin su sa maka albarka, wataƙila ma su zage ka bayan idonka alamun ba su gode ba.
0 Comments
Post a Comment