Scholarship wani tallafi ne na karatu da ake bawa dalibi, kuma akan same shi tun daga Matakin Primary har izuwa Digirin Digirgir (Wato Doctor of Philosophy, ko kuma kace Ph.D)
Scholarship ko tallafin Karatu ya kasu kashi daban-daban, kuma nau'uka daban-daban.
1• Internal/National Scholarship:
Wannan tallafi ne da gwamnatin tarayya ko gwamnatin Jiha ko ta Karamar hukuma take bada shi ga dalibai a matakai daban-daban domin fadada ilimin su.
Zai iya yuwuwa idan ka samu wannan tallafin ya zama za'a tura ka wata kasa ne kaje kayo ko karo Karatun, kamar yadda gwamnatin tarayya dana jihohi da dama suke yi.
Ta iya yuwuwa kuma idan ka samu tallafin ba wata kasar zakaje ba, anan gida ne zakayi karatun ka, kamar yadda gwamnatin tarayya take yi dama sauran wasu jihohin.
Hakanan zai iya yuwuwa idan ka samu tallafin ya zama wasu kudi ne za'a baka da zai dan rage maka radadin talaucin dalibtaka, kamar yadda gwamnatin Kano, Kaduna Suke yi.
Ko kuma a'a, za'a biyaka kudin registration dinda ka kashe ne, kamar yadda gwamnatin Kebbi take yi.
Ko kuma kyauta zakayi karatun naka har ka gama kamar yadda gwamnatin Jigawa take yi.
2• Company Scholarship:
Tallafi ne da Kamfanoni a Nigeria suke bada shi ga duk dalibin da ya cika sharudan da suka gindaya, shima ta iya yuwuwa wata kasar ne zasu kaika, ko kudin Registration zasu biya maka, ko kuma wasu kudi ne kawai zasu baka.
3• NGOs, Foundations and Individuals Scholarship:
Shima wannan wani nau'in tallafi ne da Kungiyoyi, gadauniyoyi dama daidaikun mutane suke bada shi ga dalibai, shima bayanin sa kamar na Company Scholarship ne.
4• Institutional Scholarship/ VC's Scholarship:
Wannan Shima wani nau'in tallafi ne da Jami'o'i a Nigeria suke bada shi, mafi yawanci ga daliban da suka samu maki mafi girma a matakin Degree din su, ko kuma a karshen Zangon karatu suka samu maki (CGPA) daya kai 4 Point zuwa sama.
Wannan zata iya yuwuwa Jami'ar ta tura ka wata kasa ko wata Jami'ar anan gida Nigeria kaje ka karo karatun, ko kuma ta barka a cikin ta kayi karatun, ko kuma ta baka wasu kudade, kamar yadda Jami'ar Bayero dake Kano take yi.
5• International Scholarship:
Tallafi na Kasa-da-Kasa. Shima wannan tallafi ne da kasashen duniya suke bada shi ga dalibai. Mafi yawancin wannan tallafin dalibi yakan tafi kasar da ya samu tallafin ne yayi karatu a can, basu fiye bada kudi ba.
Sannan shima ya kasu kashi-kashi, akwai wanda kudin karatun ne kawai za'a biya maka, kaikuma zaka biya kudin Abincin ka, wurin kwanan ka da sauran su, akwai kuma wanda su zasu baka har da wurin kwana amma banda abinci, akwai kuma wanda komai zasu dauke maka kawai kaidai karatun suke so kayi, ya danganta dai da yanayin tallafin.
TO AMMA ME YASA DALIBAI DA DAMA A NIGERIA SUKE FADUWA JARABAWAR ?
A iya binciken da nayi, faduwar yana da alaka ne da yaren turanci, idan ya zama kasar da zakayi karatun da yaren turanci suke amfani a gwamnatance.
Dalili kuwa shine, daliban mu sukan kasa bambancewa tsakanin turancin Ingila da kuma na America, walau wurin rubutu, idan Jarabawar a takarda ne zasuyi, walau kuma wurin fade da baki, idan ya zama Jarabawar zasu yita ne Verbally.
Akwai Kalmomi da dama da Vocabularies har ma da grammar da ake samun bambanci tsakanin turancin Ingila Dana America, to duk lokacin da kazo ka cakudasu (Kana cikin yin turancin America kuma sai ka koma na Ingila) to hakan zai sanya ka fadi Jarabawar saboda ba'a hadesu tare, tunda dai kowanne daga ciki duniya ta yadda dashi, to dole sai dai kayi daya. Idan American ne to American, idan kuma Ingilan ne to Ingilan kawai.
Misali:
Idan ka dauki turancin America su suna furta Kalmar “Matter” ne kamar haka “Meddar” wato mafi yawan wurare harafin “t” a turancin America sukan furta shi ne da sautin “d” yayin da shikuma Ingilan ba haka bane.
Haka wurin Rubuta Kalmar Colour” Misali, a turancin America ba haka suke rubuta ta ba, su suna Rubuta ne kamar haka: “Color” haka ma Kalmar “Favour” a turancin America haka suke Rubuta ta wato “Favor” so, idan kazo kanaita cakudawa to zai iya sabbaba maka faduwa Jarabawar, Allah ya kyauta.
Bissalam
Shehu Rahinat Na'Allah
18th July, 2021.
0 Comments
Post a Comment