Wani mai aikin gadi mai suna Kabiru Bappah Algus, ya kashe ubangidansa Alhaji Abubakar Muhammad (Buba Kinchiko) mai shekaru 50 ta hanyar daba masa wuka a kirji.
Lamarin ya auku ne a kauyen Malala dake karamar hukumar Dukku dake jihar Gombe.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, Alh Buba Kinchiko ya kai ziyarar bazata zuwa gonar sa domin duba mai gadin sa shin yana gudanar da aikinsa ne ko kuma ba ya yi.
A zantawar da RARIYA ta yi da dan uwan mamacin, Buhari Ahmed, ya shaida mana cewa, dan uwansa ya noma wake kuma ya dauki hayar mai gadi domin ya rika kula da barayin wake masu zuwa gonaki.
Ya kara da cewa, “Dan’uwan na ya bar gida ne da misalin karfe 12 na daren ranar Litinin a kan babur din sa zuwa gona, isar sa gonar ke da wuya, sai ya kama Mai gadin shi idon sa yana masa satar waken da ya ba shi gadi, kwatsam sai ya yi kan mai gadi isar sa kenan sai suka fara kokawa daga bisani ya daba masa wuka nan take ya mutu har lahira.
"Sai dai mai gadin ya amsa laifin da ya aikata, ya kara da cewa, bayan ya kashe shi ya gar zaya gidajen 'yan uwan mamacin ya sanar da su cewa, ba da gangan na daba wa Alhaji wuka ba, nina dabawa Alh wuka a kirji" inji mai gadin.
Nan take iyalen mamacin suka gar zaya zuwa inda abin ya faru, suna isa suka iske Alhaji cikin jini a saman wake."
Buhari Ahmed ya ci gaba da bayyana cewa, da mai gadin da iyalan marigayin duk 'yan uwan juna ne, haka zalika kuma makwabtan juna ne.
Zuwa yanzu dai mun samu labarin cewa ‘yan sandan yankin sun cafke mai gadin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Gombe.
Haka zalika Mahid Muazu Abubakar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Oqua Etim ya bayar da umarnin a mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike.
0 Comments
Post a Comment