Uwar gidan ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar NNPP, Injiniya Nura Khalil, Hajia Farida Barau ta bayyana cewa jam'iyyar NNPP jaririya ce ba ta da haƙƙin kowa a kanta kuma duk wanda ke cikinta mutumin kirki ne masu zimmar kawo gyara da son cigaban kasarmu Najeriya da kuma jihar Katsina ne.


Hajia Farida Barau ta bayyana haka ne a wajen gangamin mata masu son kawo canji a jihar Katsina domin kaddamar da manufofi da tsare-tsaren jam'iyyar NNPP a babban ofishin yaƙin neman zaben Injiniya Nura Khalil dake Katsina jiya Lahadi.


Uwar Marayun Katsina ta kara da cewa jama'a lema ta yage, tsintsiya ma ta watse, an dora mana yunwar dole, wanda ake so a yi amfani da ita a wannan lokacin kuma ba za mu yarda ba, abinda ake wa talakkawa ya ishe mu, amma wannan jam'iyyar NNPP za ta kawo sauki ga yan Najeriya da jihar Katsina cikin yardar Allah.


Hajia Farida Barau ta cigaba da cewa maigidana Injiniya Nura Khalil ya dade yana taimako masu karamin karfi a jihar Katsina, ga shi da tausayi da sanin ya kamata, bai taɓa rike mukamin kansila ba amma ya san hanyarsa ta neman kudinsa, a cikinsa yake diba yake taimakon al'umma. Gidauniyar Injiniya Nura Khalil ta fi shekara goma ta na gudanar da ayyukan jin kai a lunguna da sakon jihar Katsina ba tare da gajiyawa ba, to ina ga ya samu damar wadda zai taimake ku da kudin ku, ga shi bai iya cin haƙƙin kowa ba, babban burin Injiniya Nura Khalil shi ne taimakon mata da matasa.


Don haka ku fito kwanku da Kwarkwatarku, ku zaɓi yan takarar da jam'iyyar NNPP, mai kayan marmari ta tsaida, saboda ko a aljanna ma ana alfahari da kayan marmari, don Allah don annabi al'ummar Najeriya da jihar Katsina ku jarraba mu, saboda tsintsiya ta ce za ta share barnar da PDP ta yi, shin ta share barnar? Don mi za mu sake zabarta? Don Allah al'umma mu zabar kanmu dai-dai, Ita ce NNPP za ta kawo sauki ga al'ummar jihar Katsina da Najeriya baki daya.


Shima da yake na sa jawabin dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar NNPP, Injiniya Nura Khalil ya sha alwashin bai wa Mata dubu talatin da hudu jari a kowane wata a jihar Katsina, idan Allah ya sa ya zama gwamnan jihar Katsina a zaben 2023.