Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai tare a babban birnin tarayya Abuja ba bayan ranar 29 ga watan Mayun 2023 domin kada ya shiga cikin harkokin mulkin magajinsa.


Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mazauna babban birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin Ministan Abuja, Mohammed Bello, wadanda suka kai masa ziyarar bikin Kirsimeti a jiya Lahadi a fadar shugaban kasa, Abuja.


A wajen bikin Kirsimeti na karshe da ya yi da  al’ummar babban birnin tarayya Abuja, shugaban ya jaddada cewa zai dawo garinsa Daura na jihar Katsina a karshen wa’adinsa.


A cewarsa, matakin da ya dauka na kin mayar da Abuja ta zama mazauninsa dindindin shi ne ya baiwa magajinsa damar gudanar da harkokin gwamnati ba tare da katsalandan ba.


Shugaban ya kuma shaida wa al’ummar babban birnin tarayya cewa bai gina sabon gida a Daura ba ko kuma a ko’ina ba, kuma yana fatan ya zauna a gidan na sa kwaya É—aya na tsawon shekaru.


Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ya ce ya dade yana rike da mukamin minista saboda gaskiya da kwazonsa.