Hukumar zabe INEC ta ce wadanda suke siyan katin zabe suna da tanadin hukunci zaman gidan yari da biyan tara.
Democratic Hausa ta tattaro cewa Kwamishinan INEC na jihar Jigawa, Farfesa Muhammad Lawal Bashar ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Kwamishinan ya ce hukumar zabe ta shirya tsaf domin gudanar da dukkan zabukan ta hanyar amfani na’urar BVAS domin tabbatar da sahihin zabe.
” Na’urar za ta tantance wadanda za su kada kuri’a kuma wadanda suka yi rajista fiye da sau daya ba za su iya kada kuri’a ba.
Farfesa Muhammad ya ce Hukumar ta karbi katunan zabe na dindindin sama da dari da hamsin da shida wadanda ake ci gaba da rabawa har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023.
Ya shawarci wadanda suka yi rajista amma ba su karbi katin zabe ba da su zo su karba kafin ranar rufewa.
Kwamishinan ya kara da cewa hukumar ta yi kyakkyawan tsari da zai baiwa masu bukata ta musamman da tsofaffi da mata masu juna biyu damar kada kuri’a cikin sauki.
0 Comments
Post a Comment