Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa 19 da suka halarci bikin auren jinsi.
Kakakin ta, Lawan Ibrahim ne ya bayyana a yau Talata a Kano cewa matasan sun hallara ne domin shaida daurin auren wasu mutane biyu da ake zargin 'yan luwadi ne Abba da Mujahid.
Ya ce an yi kamen ne bayan da wani matashi nagari ya bai wa hukumar rahoton auren jinsin.
Ya ce tuni Jami’an hukumar da ke hedikwata a Sharada Kano, su ka isa wurin kafin a fara daurin auren su ka kuma tashi taron.
"A cikin wadanda aka kama akwai mata 15 da maza hudu," in ji Ibrahim.
“Abba da Mujahid sun tsere nan take jami’an Hisbah su ka isa wurin daurin auren, amma mai shirya bikin, Salma Usman, ‘yar shekara 21, tana hannunmu.
“Wadanda aka kama za a mika su ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace kamar yadda akasarin matan suka ce an gayyace su zuwa daurin auren ne daga jihohin makwabta.
"Za mu kara kaimi wajen ganin an kama Abba da Mujahid," in ji shi.
Ibrahim ya jaddada cewa hukumar ta kudiri aniyar kawar da duk wata munanan dabi’a a jihar.
0 Comments
Post a Comment