Anyi taro domin tabbatar da zaman lafiya a Lokacin babban zabe Mai zuwa Amma an nemi Gawuna da Garo an rasa..
A jihar Kano yau ne kungiyoyin masu zaman kansu Suka gudanar da Taron tabbatar da zaman lafiya domin gabatowar zaben shekara ta 2023 a jihar Kano. Karkashin jagorancin hukumar Yan sanda ta jihar Kano tare da tallafin Aminu Magashi Foundation, Adamu Gwarzo Foundation, Arewa Agenda da sauran kungiyoyin tabbatar da zaman lafiya da tallafi. Wanda aka gabatar a dakin taro na Lebanon Club dake Bompai a ranar Talata 20 ga watan disamba 2022. Hoto: Sani Maikatanga.
Sai dai a taron na Zaman lafiya Dan takarar Gwamnan jihar Kano Dakta Nasir Gawuna da Mataimakinsa ba Sami halartar taron ba duk da cewa taro ne Mai mahimmanci, Duk da cewa sun tura wakili amma jama'a da dama na CeCe kuce game da rashin zuwan su taro..
0 Comments
Post a Comment