“Wani zankaɗeɗe matashi mai suna Abba Gibirima Al-dabaiba ɗan asalin ƙasar Libya kuma haifaffe, mai sana'a canjin kuɗi a ƙasarsa, ya koka ganin yadda Ƴan mata ba su taɓa nuna ko'in kula akansa ba a dalilin ƙulla wata abota ba.”
“A cewar matashin, ga shi fari, dogo, irin wanda mata suka fi so; amma abin ban haushi tinda yake babu mace wacce tataɓa cewa Tana sonsa, ko wacce tataɓa cewa “Abba turo min da kati, bisani dai Ƴan matan basa iya Soyayya da shi bare su yaudaresa, kuma shi ruwa a kallo neman budurwa yake ido rufe.”
“Matashin ya faɗin hakanne a yayin Zantawarsa da Jaridar Alfijir Hausa a jiya Talata ta wayan tarho daga ƙasar Libya ɗin, kuma matashin ya buƙaci a isarwa Duniya saƙonsa ko zai samu wacce take sonsa, kuma a shirye yake ka kashe mata maƙudan kuɗi.”
Gare ku masu karatu Shin wani irin shawara zaku bawa Matashi Abba Gibirima mai garin kuɗi ?
0 Comments
Post a Comment